[News]Adam A Zango Yayiwa Yara Da Kannensa Allah Ya Isa

Kamar yadda kuka sani a Kwanakin Baya Rikici yaso barkewa a tsakanin Manyan jarumai Adam A Zango Da Ali Nuhu wanda Hakan yasa yaransu suketa zage zage da cin mutuncin juna kafin daga bisani a sasanta lamarin.Wanna dalili ne yasa jarumi adam a zango yafito yayi Allah ya isa ga yaransa dakuma kannensa Akan duk wanda yasake daukar wani mataki akan wani zageshi ya wallafa Wannan jawabi ne a shafinsa na instagram ga bayanin Nasa kamar haka.

“DAGA YAU DUK WANDA YA KARA RIGIMA KO HAYANIYA AKAN AN ZAGENI KO AN ZAGI IYAYENA A CIKIN KANNE NA, ABOKAINA DA YARANA….ALLAH YA ISA BAN YAFE MASA BA……”