Cikakken Tarihin Jarumi Ali NuhuAli Nuhu Mohamamed wanda aka haifa a ranar sha biyar ga watan Maris na alif dari tara da saba’in da hudu (15 March 1974), Jarumi ne na fina-finai da suka hada da na Hausa da kuma Turanci, sannan kuma ya kasance mai bada umarni wajen shirin fina-finan Hausa, yakan taka rawa da kuma rubuta fina-finai.
Jarumi Ali Nuhu yayi fice a matsaki daban-daban wnda ma wasu da dama kan kalle shi a matsayin kwarzo kuma haziki wanda ya dauki lambobi yabo dana girma da suka haura na duk wasu Jarumai a cikin masana’antar ta fina-finan Hausa.
Ali Nuhu ya kasance Jarumi na farko da ya fara fitowa a fina-finan kudancin Najeriya wanda a cikin su suka hada da “Sitanda” da kuma “Last Fligh to Abuja” . A lokutan fitowar sa a cikin wadansu fina-finai na Turanci, Jarumi Ali ya samu suka daga bangarorin al’umma musamman ma ta yadda yakan yi dabi’u da suka sabawa al’adar Hausa wacce ya fito daga bangaren ta,
An haifi Jarumi Ali Nuhu a garin Maiduguri dake cikin jihar Borno a Najeriya.
An haifi Jarumi Ali Nuhu a garin Maiduguri dake cikin jihar Borno a Najeriya.

Mahaifinsa mai suna Nuhu Paloma ya fito ne daga shiyar Balanga ta jihar Gombe a Najeriya. Mahaifiyarsa Fatima Karderam Digema ta fito ita kuma daga shiyar kauyen Bama a jihar Borno.
Nuhu yayi mafi yawan shekarun sa na kuruciya a birnin Kano. Ya halarci makarantar firamare ta Riga da ma makarantar Sakandare duka a jihar Kano. Nuhu ya kasance mai rike da takardun digiri daga Jami’ar Jos inda ya karanta ilimin kasa (Geography).
Ali ya samu halartar wadansu makarantu inda yayi gajeren karatu domin koyar fannin shirin fim. A cikin wadan nan makarantu akwai Jami’ar Kudancin Califonia dake kasar Amurka.

Jarumi Nuhu ya kasance yana da aure inda yake tare da matarsa mai suna Maimuna Ja-AbdulKadir inda suka da ‘ya’yansu biyu da suka haka da Fatima da kuma Ahmad.
Jarumi Ali Nuhu ya shiga masana’antar shirya fina-finai a shekarar alif dari tara da casa’in da tara (1999) wanda yayi fice a cikin wani shirin fim mai suna Sangaya. Jarumi Ali ya samu kansa a cikin shirin fina finai masu dumbin yawa wadanda akalla yawansu ya haura 300. Fina finan Jarumi Ali na yaren Hausa sunfi yawa. Sai dai bangaren na Turanci ma ba’a barshi a baya inda ya fito a fina finai masu yawa ciki harda shahararren fim fin nan mai suna Sitanda