Dalilin Dayasa Nayi Aure Sau 7 – Inji Sadiya KabalaJarumar Finafinan Hausa  Sadiya Kabala, ta bayyana cewa abin da yasa ta yi aure sau 7 a cikin fim din ‘Kwadayi da Buri’ domin ta nuna illar son abin duniya ga ‘yan matan wannan zamanin.
Jarumar, wadda ta fito da sunan Salmah a fim din, ta yi aure barkatai sakamakon kawayen banza, da ta ke dasu wadanda suka rika bata mummunar shawara.


A cewar ta abin da yasa ta fito da wannan halin, domin ta nunawa masu wannan burin a zuciyar su cewa shi fa kwadayi mabudin wahala ne, kuma da mai kudi da talaka, dukansu Allah ya yi su, Allah zai iya azurta wanda yaso a lokacin da ya ga dama, kuma zai iya talauta wanda yaso a lokacin da ya ga dama.

Daga karshe ta shawarci ‘yan uwanta mata da su zamo mutane na gari.

Hausa9ja.Ga Posted