{News} Buhari Ya Yabama Agameda Juriyar Saraki A Shari’arsa


Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya mayar da martani game da wanke shugaban Majalisar Dattawa Sanata Bukola Saraki da kotun koli ta
yi.
Shugaban ya ce duk da kalubalen da bangaren shari’ar kasar ke fuskanta amma hakan ya nuna bangaren na aiki sosai, kuma babu wanda za a bari ya karya tsarin.
Shugaban ya fadi haka ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun mai magana da yawunsa Malam Garba Shehu.
“Na ga shugaban Majalisar Dattijai Bukola Saraki ya bi tafarki mafi wahala na bin matakan shari’a, ya jure, kuma daga karshe kotun koli ta ce ba ya da laifi” in ji shugaban.
Ya kara da cewa: “Akwai wasu lokutta da dama da wasu mutane cikin rashin tunani suke neman kawo lalaci ga bangaren shari’a duk don su kare
kansu, maimakon mayar da hankali ga bin matakan da za su wanke kansu.”