AN GANO MAKARKASHIYA DA AKA KITSA DON MURDA ZABE 2019Sakamakon gano wata makarkashiya da aka kitsa a kan zabe hukumar zabe ta Kasa wato INEC ta tura rubutaccen takarda wa shugabannin zabe na jihohi take umartansu da su dawo da dukkan na'uran tantance katin zabe wato "Card Reader" da aka raba a kananan hukumomi domin a sake canza tsarin aikin na'urar saboda tsoron kar anyiwa na'urorin kutse

Allah Ka ba mu hakuri, can watannin baya lokacin da muke bayanin shirin da akayi don ayiwa na'urorin zabe na Kasa kutse (hacking) a canza bayanansu sai aka samu wasu makafi daga cikin masoya Buhari suna karyata yiwuwar hakan, alhali sun manta hatta Kasar Amurka da take takama da ilmin na'ura mai kwakwalwa a duniya da tsaro sai da aka yiwa na'urorin zaben Kasar kutse

Lallai ya kamata 'yan Nigeria mu dage da addu'ah, Allah ne Kadai Ya san mugun shirin da makiya zaman lafiyar Nigeria sukayi

Muna rokon Allah Ya kawo mana dauki.


#Hausa9ja Reports

Promote Your Music
Call/WhatsApp +2348103302990


Post a Comment

0 Comments