[New] Dalilin Daya hana Neymar barin PSG

Bayan watanni da aka dauka ana sa-toka-sa-katsi da kuma ka-ce-na-ce yanzu dai mun ga karshen abu. Neymar zai ci gaba da zama a Paris St-Germain.
Yayin da kura ke lafawa, ya kamata mu sani cewa ba Neymar ne wanda abin ya fi bai wa mamaki ba - duk da kokarin da ya yi na barin kungiyar, ya kwana da sanin cewa wannan cinikin ba mai yiwuwa ba ne.
Gidan rediyon El Chiringuito na kasar Portugal ya ruwaito cewa Neymar ya yi kuka da idonsa bayan an shaida masa cewa ba zai koma tsohuwar kungiyarsa ta Bercelona ba.
SUBSCRIBE HAUSA9JA Tv ON YOUTUBE

 Babban abin da ake nema yayin kulla yarjejeniyar ciniki - a harkar kwallo ko kuma a ko'ina - shi ne ko dai a samu mai zumudin saya ko kuma mai zumudin sayarwa, ko kuma in so samu ne a samu duka.
Sai dai a wannan yanayin, ita Bercelona ta yi zargin cewa zakarun na Faransa tun asali ba su da niyyar sayar da dan wasan, yayinda ita kuma PSG tana zargin cewa Berca ba tun farko dama bata yi niyyar sayan dan wasan ba ne.
Wannan rashin yardar shi ne abin da ya gurgunta tattaunawar tun daga farkonta

Promote Your Music
Call/WhatsApp +2348103302990

Post a Comment

0 Comments