Kasar China zata sake rubuta Bibul da Qur’ani don su ‘daidaita da zamani


- Kasar China zata sake rubuta Bibul da Qur’ani don su ‘daidaita da zamani’ 
- Hakan ya biyo bayan durkushewar kungiyoyin addinai na kasar ne da hukumomi suka lura dashi 
- Za a kara rubuta littafan addinan ne tare da sauya wasu layika da suka ci karo da tanadin jam’iyyar mutane Kasar China zata sake rubuta Bibul da Qur’ani don su ‘daidaita da zamani’ sakamakaon durkushewar kungiyoyin addinai na kasar, wani rahoto ya bayyana. 

Sabbbin littafan addinan ba zasu kunshi wasu abubuwa da suka ci karo da dukkan tanadin jam’iyyar jama’a ba, daya daga cikin manyan jami’an jam’iyyar ya sanar. Sakin layukan da suka ci karo da tanadinsu za a gyara su ko kuma a kara fassara su. 


Duk da cewa, ba a kira Bibul da Qur’ani kai tsaye ba, jam’iyyar ta yi kira a kan gyara a littafan addinan kasar, wadanda abinda suka kunsa bai yi dai-dai da cigaban zamani ba.
An bada wannan umarnin ne a taron da aka yi a watan Nuwamba wanda shugaban kwamitin kabilu da addinai na kasar ya shugabanta. 
An yi taron ne sakamakon kalubalen da kasar China ke fuskanta a kan dokokinta na addini. 
Wani bidiyon sirri da ya bazu cikin kwanakin nan ya bayyana yadda gwamnatin kasar China ke wanke kwakwalwar musulman yankin Xinjiang don sun rungumi al’adar turawan kudu. Fallasar nan kuwa ta sa sakataren Amurka Mike Pompeo a watan Nuwamba ya ce, hakan na bayyana cewa hukumomin kasar na tirsasawa musulmin yankin sakin addininsu.

Post a Comment

0 Comments