Kungiyar Tarayyar Turai na tsaka mai wuya kan coronavirusAna ci gaba da samun rabuwar kai tsakanin kasashen Turai mambobin kungiyar Tarayyar Turai wato EU da kuma cibiyoyi a kan yadda ya kamata su bullowa annobar Covid-19, yayin da cutar ke ci gaba addabar duniya baki daya:
  • Bayan tattaunawar awa 16, ministocin kudin kasashen kungiyar sun fada a yau Laraba cewa har yanzu ba su cimma matsaya ba kan matakin za su dauka game da tattalin arzikinsu. Kasashen Jamus da Netherlands suna fargabar cewa za su bige da daukar nauyin bashin wasu kasashen, yayin da kasashen Italiya da Spain suka ce har yanzu akwai jan aiki
  • Babban jami'in lafiya na kungiyar ta EU ya ce ba shi da wani kwarin gwiwa a kan kungiyar game da matakan da take dauka kan annobar coronavirus
  • Wasu kotuna a kasar Jamus sun yi watsi da bukatar wasu 'yan darikar Katolika ta zuwa bikin Easter yayin da ake tsaka da dokar hana fita a kasar
  • Shi kuwa Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya sha caccaka ne bayan ya kai ziyara wani gari da cutar ta yi wa kamari, inda mutanen garin suka fito domin gaishe shi. Rahotanni sun bayyana cewa Macron ya yi ta rokon su da su bai wa juna tazara amma ko a jikinsu

Post a Comment

0 Comments