Mutum bakwai sun warke daga coronavirus a AbujaPMinistan Babban Birnin Tarayyar Najeriya Abuja, Muhammaed Bello ya ce suna gab da sallamar mutum bakwai da suka yi jinyar Covid-19 a Abuja bayan gwaji ya nuna sun warke daga cutar.
Ministan ya bayyana haka ne a wata sanarwa da ya aike wa manema labarai ranar Talata. Ya kara da gode wa mazauna birnin game da "hadin kan da suka bayar" wajen bin dokar hana fita da aka saka.
A gefe guda kuma, Minista Muhammad Bello ya kai ziyarar gani da ido wata cibiyar killace masu coronavirus mai cin gado 500, wadda bankin Polaris Bank Plc ya sadaukar ga hukumar birni
Cibiyar killace masu coronavirus a Abuja
Ita ma FATE Philanthropy Coalition for Covid-19 - kungiya mai yaki da Covid-19 - ta bayar da tallafin irin wannan cibiya mai gado 50. Kazalika akwai asibitoci biyu da aka tanada domin kulawa da masu cutar da suke a Asokoro da kuma Karu.
Har wa yau, sanarwar ta zayyana wasu lambobi da ta ce na kiran gaggawa ne domin bayar da rahoton wanda ake zargin ya kamu da cutar - 08099936312, 08099936313.
Tun asali dai wadanda suka kamu da coronavirus a Abuja ana killace su ne a asibitin koyarwa na Jami'ar Abuja da ke Gwagwalada.
Zuwa yanzu, akwai mutum 50 da aka tabbatar sun kamu da Covid-19 a birnin na Abuja - adadi na biyu kenan mafi yawa bayan Jihar Legas.
Jumullar wadanda suka kamu da cutar a Najeriya sun kai 254, a cewar hukumar NCDC mai yaki da yaduwar cutuka. Mutum 44 daga ciki sun warke, yayin da shida suka mutu.

Post a Comment

0 Comments